Hedkwatar Tsaro ta yi watsi da hotuna da bidiyo da ake ta yadawa da ke nuna yadda ake jibge gawarwakin mutane a cikin manyan kaburbura wadanda ake zargin gawarwakin mutanen ne da aka kashe a yayin harin sojoji.
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Benjamin Sawyerr, shi ne wanda ya yi watsi da hotunan da bidiyon a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.
Sawyer ya ce hoton da ke dauke da taken, “Alhamdulillah, Zamfara dole ta samu zaman lafiya” da wasu hotuna da bidiyo a mummunan kama wadanda ake nuna cewa sun fito ne daga ayyukan da sojojin da suke yi a a sassan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na kasar ba gaskiya bane.
A cewarsa, ya ce yana da kyau a bayyana cewa wadannan hotunan ba gaskiya bane; “zargin karya ne kuma ba shi da wata alaƙa da ayyukan da rundunar sojan Nijeriya ke gudanarwa a halin yanzu”, ya tabbatar.