Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta mayar da martani kan hukuncin da mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke a yau 29 ga watan Nuwamba, inda ta yanke wa Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni uku saboda kin bin umarnin kotu.
Olajuwon ya yanke wannan hukunci ne biyo bayan karar da Patrick Okoli, tsohon dan sandan ya shigar, inda ya ce ya yi ritaya daga aikin ‘yan sandan Najeriya ba bisa ka’ida ba kuma tilas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Yasa ‘Yan Daba Suke Kai Hari Tare Da Kona Ofishin INEC — Shehu Sani
A cewar takardar shaidar da ke goyon bayan karar, mai neman ya yi murabus ne da karfin tsiya a watan Yunin shekarar 1992. Bayan ya kalubalanci ritayarsa ta karfi, wata babbar kotu a jihar Bauchi a ranar 19 ga watan Fabrairun shekarar 1994, ta yanke hukunci a kan wanda ya nema tare da soke takardar murabus din tasa ta dole.
Da yake mayar da martani kan hukuncin da aka yanke wa IGP, kakakin rundunar ‘yan sandan CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce ofishin sufeto-janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba Alkali bai yi watsi da umarnin kotu ko kin bin doka da oda ba, domin ba shi da masaniya.
Bayanin na bangaren sanarwar yana karanta cewa;
“Yana da kyau a lura cewa lamarin ya shafi jami’in da aka kora tun a shekarar 1992, shekaru kadan bayan IGP na yanzu ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya, bisa la’akari da hujjojin da aka samu daga rahotannin.
An yanke hukunci na baya-bayan nan game da lamarin a shekarar 2011 wanda bai kamata ya kasance karkashin kulawar hukumar ta rundunar ta yanzu ba. Don haka, labarin yana da ban mamaki.
Sai dai IGP din ya umurci kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashin shari’a na rundunar da ya binciki zargin da ake yi masa a kokarin tabbatar da matsayin kotun da kuma ba da shawara ta fuskar shari’a domin IGP ya gaggauta daukar matakin da ya dace.
Sufeto-Janar na ‘yan sanda ya nanata kudurin sa na bin doka da oda tare da hada kai da bangaren shari’a don tabbatar da gaggauta aiwatar da shari’a domin inganta tsarin shari’ar laifuka.”
A wani labarin kuma, Gwamnatin Zamfara Ta Gargadi Jam’iyyar PDP Akan ‘Yan Bangar Siyasa
Gwamnatin jihar Zamfara ta gargadi jam’iyyar hamayya ta PDP da kar ta sa ‘yan bangar siyasa a matsayin dabarun da za ta bi domin ganin ta ci zabe a jihar.
A zantawarsa da manema labarai mataimakin gwamnan jihar, Sanata Mohammed Nasiha, a gidan gwamnatin Gusau, ya zargi jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na gwamna da yin amfani da ‘yan barandan siyasa wajen kaddamar da hare-hare kan allunan talla da kadarori na ‘yan jihar da ba su ji ba ba su gani ba.