Hisbah A Zamfara ta yunƙuro kan yaƙi da Ƴan bindiga, ta haɗa hannu da NSCDC
Hukumar Hisbah ta jihar Zamfara ta ce za ta hada kai da jami’an tsaron farin kaya na Najeriya NSCDC a jihar Zamfara domin tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban Hukumar Alhaji Ashahabu Zoma ne ya bayyana haka, wanda ya jagoranci gudanarwar hukumar a ziyarar ban girma da ya kai ga Hukumar NSCDC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Muddin Aka yi Sahihin ZaɓeAPC za ta sha Kaye – Wike ya mayar wa Buhari martani
Shugaban hukumar ya nanata cewa hukumar tsaro ta Civil Difens ta samu wani matsayi mai girma a cikin al’umma kuma ta tabbatar da cewa ita Hukuma ce mai cikakken mutunci da ɗa’a.
Zoma ya bayyana cewa rundunar ta nuna matukar hadin kai da hukumar Hisbah a baya, wanda ya sanya suka zo neman wata hadin kai.
Ya bukaci a ci gaba da gudanar da irin wannan aiki a karkashin jagorancin Kwamandan, A Sparks.
Da yake mayar da martani, Sparks ya tabbatar wa Hukumar da kyakkyawan hadin gwiwa da aiki tare yayin da hukumomin biyu suka fita kan manufa iri daya a jihar.
Shugaban NSCDC na jihar ya hori Hukumar da ta tabbatar da kulla alaka mai kyau tsakanin sauran hukumomi domin gudanar da ingantaccen aiki.
A wani labarin kuma: Ƴan Sanda sun kama Ƴan daba 22 da suka Farmaki Ƴan Banga a Bauchi
Rundunar Ƴan sandan jihar Bauchi ta kama wasu ‘yan daba 22 da ake zargin sun kai hari tare da raunata wasu ‘yan banga a cikin babban birnin Bauchi ranar Alhamis.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Wakil, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa Manema Labarai a Bauchi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta, 2022.