Hukumar kula da Hisbah ta bayyana cewa ta ƙwace Kwalabanin Giya 1,906 a samamen data kai da dama a Jahar a shekarar 2021.
Kwamandan Hisbah na Jahar Ibrahim Ɗahiru ya bayyana haka a lokacin da yayi jawabi da Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya a Dutse a ranar Talata.
Ɗahiru yace an kama Kwalabanin giyar a lokacin da suka kai wani samame wanda Jami’an su yakai a mashaya da Otel a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Hatsarin Mota Ya Yi Sana Diyyar Mutuwar Mutane Biyar A Gaya Dake Jihar Kano
Yace an kama waɗanda ake zargi da shan giyar da suka haɗa da Mata Masu Zaman Kansu a dalilin wannan mummunan aiki.
Ɗahiru ya jaddda cewa, shan giya haramun ne a tsakanin musulmi a Jahar, inda ya buƙaci mazauna da su guji yin hakan da sauran wasu ayyukan ashsha dake da manufar lalata al’umma.
Ya bayyana cewar giyar da aka amshe, da kuma waɗanda aka kama an miƙa masu ga ƴan sanda domin ɗaukar mataki.