Hisbah ta ƙwace kwalaben barasa 384 a Jigawa
Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta kama kwalaben barasa 384 a karamar hukumar Kazaure.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƙarancin Sani ne Zai sanya Karamin Ministan Buhari Fadin Bakar Magana ga Atiku – Phrank
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Rundunar, Muhammad Sale Korau ya sanya wa hannu a ranar Litinin.
Ya ce jami’an da suke sintiri karkashin jagorancin kwamandan jihar Ibrahim Dahiru sun samu nasarar cafke barasa a kan hanyar Katsina zuwa garin Kazaure.
Korau ya ce an kama mutum guda da laifin safarar barasa a jihar.
Ya ce an mika wanda ake zargin ga ƴan sanda domin gudanar da bincike kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukuncin doka.
Sai dai ya yabawa al’ummar jihar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bayarwa wajen yaƙi da munanan ɗabi’u a cikin al’umma.