Hukumar Hisbah reshen jahar Kano a ranar Alhamis ta ce ta cafke 27 a babban birnin jahar Kano a kan zargin sabawa dokar hana bara a jahar.
Kakakin rundunar Hisbah reshen jahar Kano, Malam Lawan Ibrahim, ya bayyana hakan a yayin da ake hira da shi.
Ibrahim ya ce an kama mabaratan ne da misalin karfe 12:00 na rana zuwa 2:00 a ranar Alhamis a kusa da Kano Guest Inn da ke unguwar Sabon Gari a ta yankin Triuph da kuma Railway.
Ya ce a cikin an kama maza 18 da mata yara 9 wadanda shekarunsu ke tsakanin shekaru 13 zuwa 19.
A cewarsa, hukumar za ta ci gaba da gudanar da aiyukar ta na kama mabaratan wadanda suka ki bin umurnin hukumar har sai an bar bara a fadin jahar.