Hukumar Kula da Harkokin Hisbah ta Jahar Kano ta kama ɗan shekara 26 Aliyu Na Idris, Wanda ya sanya kanshi domin saidawa akan kuɗi Naira miliyan 20.
Idan dai za’a iya tunawa, Jaridar Dimokuraɗiyya ta kawo maku rahoton wani yaro wanda ya kasance maɗinki, da hoton shi ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani, inda yake yawo akan Titi, ɗauke da takarda da aka rubutu kamar haka “wannan mutumen na sayar wa”.

KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun bukaci Milliyan 60 kafin sakin masu Ibada da su kayi Garkuwa da su a Neja
Haka zalika, Ƴan sandan Hisbah sun kama shi.
Kwamanda-Janar na Hukumar Hisbah Sheikh Harun Ibn-Sina ya tabbatar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da sashen BBC na Pidgin, inda yace an kama shi ne, saboda musulunci ya hana mutum ya saida kanshi.
“Dagaske mun kama shi a ranar Talata da dare, kuma ya shafe tsawon dare a tattare damu, amma bamu tuhume shi ba,” inji shi.