Jarumin fim ɗin ƙasar Amurka Chadwick Boseman, wanda ya yi shahararren fim ɗin Black Panther, ya rasu.
Sanarwar rasuwar Chadwick, ta jefa masoya da masu harka a masana’atar fim a faɗin duniya cikin alhini.
Chadwick mai shekara 43 ɗin ya rasu ne a Los Angeles sakamakon cutar kansa da ya shekara huɗu yana fama da ita.
https://dimokuradiyya.com.ng/an-karrama-fati-washa-a-ingila/
Amma bai taɓa tattauna batun rashin rafiyar tasa a bainar jama’a ba, yayin da ya ci gaba yi aikin manyan finafinan Hollywood a yayin da sau dama aka masa tiyata, kamar yadda iyalansa suka bayyana.
Sakon rasuwar da suka fitar ya ce “Chadwick, Mayakin gaske ya jure cutar har ya kawo muku fina-finai da dama da ke matuƙar ƙauna”.
Iyalan sun ce fina-finansa na Marshall, Da 5 Bloods, August Wilson’s Ma Rainey’s Black Bottom da sauransu duk an yi su ne a tsakanin lokutan da yake tsaka da rashin lafiya.