Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Gali Umar Na’abba zai amsa gayyatar hukumar tsaro ta DSS cewa ya bayyana a ofishinta.
A ranar Juma’a DSS ta gayyaci Ghali Na’abba ya bayyana a ofishinta dake Abuja a yau Litinin ɗin nan, amma babu bayani game da dalilin gayyatar.
Ghali ɗaya ne daga shugabannin sabuwar harkar siyasa ta National Consultative Front (NCFront) ta tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Farfesa Pat Utomi.
https://dimokuradiyya.com.ng/ya-kamata-a-hukunta-mailafiya-shugabannin-arewa/
Jami’in hulɗa da Jama’a na NCFront, Yunusa Tanko, a cikin wata sanarwa ya ce, “Ana sanar da ku cewa ranar Juma’a DSS ta gayyaci ɗaya daga cikin shugabannin NCFront kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Ghali Umar Na’abba, bayan hirar da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels a ranar Alhamis game da manufar NCFront na sabuwar Najeriya da za ta amfani kowa.
“Shugabanmu Ghali Umar Na’abba ya yanke shawarar amsa gayyatar kuma zai ziyarci hedikwatar DSS da ke Abuja ranar Litinin da karfe 12.00 na rana.