Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya ce horon da ya samu a Kwalejin Tsaro ta Indiya da ke Wellington na kasar a shekarar 1973 ya kasance wani bangare na nasarar da ya samu a aikin soja, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanya wa hannu, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin karamin ministar harkokin waje da majalisar dokokin kasar Indiya, Vellamvelly Muraleedharan, a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sanarwar mai taken, ‘A ganawar da ya yi da Ministan Indiya, Shugaba Buhari ya tuna kwanakin da ya kwashe a Kwalejin horaswan aikin soji dake Wellington.
KARANTA WANNAN LABARIN: Har Yanzu A Gidan Haya Nake A Abuja, Amma Ina Fatan Mallaka Nan Gaba – Shekarau
Buhari ya ce, “Wannan kwarewa ce mai kyau. Ina tsammanin ni Laftanar kanar ne a lokacin, kuma na yi shekara guda a Indiya. Mun yi balaguro kuma mun haɗu da mutanen duniya daga ƙasashe daban-daban. Ya zama wani bangare na nasarar da na samu a aikin soja.”
Ya kuma jaddada ci gaba da alaka mai karfi da ke tsakanin kasashen biyu inda ya ce ‘yan kasar Indiya ne suka kafa makarantar horas da jami’an tsaron Najeriya, kuma kasashen biyu suna da kyakkyawar alaka ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma ta fuskar tsaro.
A nasa bangaren, Muraleedharan, wanda ya bayyana Najeriya a matsayin “cibiyar huldar mu (Indiya) da Afirka, ya ce ya zo kasar nan ne domin halartar taron kasuwanci tsakanin Najeriya da Indiya.
Ministan ya kuma mika gaisuwar firaministan kasar Indiya, Narendra Modi, inda ya kara da cewa Najeriya da Indiya na da kyakkyawar alaka ta fuskar kasuwanci, tsaro, ilimi, da dai sauransu.
Ya ce Indiya a matsayinta na kasa mafi girma a dimokuradiyya a duniya a shirye take ta hada kai da Najeriya domin samun nasarar a babban zabe a shekarar 2023.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamna Buni Ya Ba Iyalan Malamin Da Aka Kashe Aiki Yi
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayar da aikin yi kai tsaye ga ‘ya’yan marigayi malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami da aka kashe a ranar Juma’ar da ta gabata a kusa da Gashua, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
Gwamna Buni ya ba da umarnin ne a ranar Talata lokacin da ‘yan uwan marigayin suka ziyarce shi domin nuna jin dadinsu kan yadda ya ke nuna damuwarsa ga iyalan.