Ma’aikatan dake aiki a dogon ginin nan da ya ruguzo da sauran al’umma gari na cigaba da tururuwar zuwa wajen da lamarin ya faru domin ganewa idanuwan su.
Ginin dai ya kasance mai hawa 20 ne, wanda ake tsaka da aikin gina shi, a unguwar Ikoyi. Kuma kwatsam sai rushewar sa aka gani ba tare da sanin dalili ba.
Kawo yanzu dai babu wani cikakken rahoto dangane da salwantar rai, ko kuma adadin waɗanda suka jikkata sakamakon rushewar ginin.
Yanzu dai anyi ittifakin cewa ginin ya danne mutane da yawa.