Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki yanzu haka suna Jos, babban birnin jihar Filato, domin kaddamar da yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Ana ci gaba da gudanar da yakin neman zaben a filin wasa na garin Ruwang Pam, wanda ya cika makil.
KARANTA WANNAN LABARIN: Saurayina Yana Bani Sama Da Miliyan N11m Don Gyara Kaina, Budurwa
Tun da farko dai wasu gwamnonin jihohi sun tarbi shugaba Buhari daga inda ya yi tattaki zuwa wurin taron.
Akalla gwamnonin jam’iyyar APC 10 ne suka halarci bikin.
A WANI LABARIN KUMA: Jam’iyyun siyasa ne ake so a yaƙa da Canja fasalin Naira – Deji Adeyanju
Shahararren dan gwagwarmayar zamantakewa da siyasa, Deji Adeyanju, a ranar Talata, ya ce sake fasalin kudin Naira da babban bankin Najeriya, CBN ya yi, don ya shafi jam’iyyun siyasa na adawa ne ya sanya aka yi shi.
Adeyanju ya ce manufar CBN ta sa ‘yan adawa su rika zagayawa da kudi tare da zabukan da za a yi.