Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ziyarci sojojin da suka samu raunuka a asibiti tare da yin alkawarin tabbatar da ci gaba da tallafawa yaki da ‘yan bindiga da duk wani aiki na ta’addanci.
Mista Matawalle wanda ke sanye da kakin soji ya ce ziyarar ta zama dole domin kara kwarin gwiwar jami’an da ke yaki da rashin tsaro.