A ranar Talata ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya isa Kano domin halartar taron tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto karo na 8.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje tare da wasu mukarrabansa da wasu mataimakan sa sun tarbi mataimakin shugaban kasar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa ana gudanar da taron tunawar ne a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnatin Kano.