By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, tare da wasu jiga-jigai, a ranar Talata, sun halarci jana’izar marigayiya Barista Angela Folarin, matar Sanata Teslim Folarin, mai wakiltar mazabar Oyo ta tsakiya.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa taron jana’izar da aka gudanar a cocin Sacred Heart Catholic Ilupeju, dake Ibadan ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.
Barista Angela Nwaka Folarin ta rasu ne a watan da ya gabata kuma an binne ta a Ibadan ranar Talata jim kadan bayan kammala jana’izar.
Tawagar ta shugaban majalisar dattijai zuwa Ibadan sun hada da mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Robert Ajayi Boroffice; Mataimakin Shugaban bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi; Kakakin Majalisar Dattawa, Sanata Surajudeen Ajibola Basiru; Sanata Ayo Akinyelure, mai wakiltar Ondo ta tsakiya; da Sanata Yakubu Oseni, mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya.