Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya ziyarci Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Fargabar Mutane 33 Sun Mutu Sakamakon Kifewar Wani Jirgin Ruwa A Jihar Neja
Atiku, wanda ya ziyarci Kaduna gabanin tattaunawarsa da kwamitin hadin gwiwa na Arewa, ya shaida wa sarkin cewa ya je fadar sa ne domin neman alfarmar sarki da kuma kusanci da shi a kan tafiyar tasa.
A wani labarin kuma, Dalilin Da Yasa Ilimin ‘Ya’ya Mata Yake Da Muhimmanci – Minista
Ministar harkokin mata,Pauline Tallen ta ce tilas ne Najeriya ta kara mai da hankali kan ilimin yara mata, saboda ana alakanta ‘ya’ya mata da kaso mai yawa na samun nasarori a harkokin ci gaban kowace al’umma.
Tallen ta bayyana haka ne a lokacin da take jawabi ga manema labarai a gefen taron Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya da kungiyar ’yan mata ta Bida (FEGGICOBIDOGA) karon farko na Duniya da Babban taron shekara-shekara na 2022 (AGM).
Ta ce ‘ya’ya mata wani bangare ne mai matukar muhimmanci a cikin al’umma, don haka akwai bukatar a karfafa su musamman ta hanyar ilimi.
A cewarta, ‘yan mata sun mamaye wani wuri na musamman a cikin gida kuma suna taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma gaba daya.
Wannan matsayi, in ji ta, ya nuna bukatar karfafa su ta hanyar shigar da yarinyar a makaranta.