Ɗalibai sun koma karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano bayan shafe watanni fiye da takwas suna zaman gida.
An buɗe jami’ar ne bayan janye yajin aikin da ƙungiyar malaman Jami’o’i ta ASUU ta yi da kuma izinin gwamnatin tarayya na buɗe makarantun bayan rufe su sakamakon annobar korona.
An ga ɗaliban sanye da takunkumi a yayin da suka koma karatu a Jami’ar Bayero a ranar Litinin.
Bbc Hausa suka wallafa hotunan.