Idan aka zo batun daukar wanka, akwai wadanda ba za su taba yarda a bar su a baya ba, Legit.ng ta ruwaito.
Wannan mutumin ya dauki hankulan jama’a bayan ya bayyana wani salo na musamman wanda babu wanda ya taba ganin irin shi.
Nan da nan mutane da dama su ka yi caa su na tsokaci iri-iri tare da yada bidiyon a TikTok, bayan ganin yadda shigarsa ta dauki hankula.
KU KARANTA: An cafke matashin da ake zargin yana damfarar mutane da katunan ATM guda 32 a Adamawa
A cikin bidiyo an ga yadda ya sanya riga da wan don atampa tare da wani matsattsen wando wanda daga gani tela ne yayi.
Sannan da yadin atamfar aka lullube motar da kuma jakar da ya rike tare da tabarau din da ke fuskarsa.
A hannunsa ma akwai wani zabgegen agog on hannu wanda idan ka kalla ka san dai kawai wanka ya bi jiki.
Kyakkyawa, mai mazaunai da albarkar ƙirji kuma ‘yar masu kuɗi nake so, Matashi na neman aure
Wani matashi mai suna Solomon Hangega daga Jihar Binuwai ya wallafa bayani akan yadda yake bukatar matarsa ta sunna ta kasance, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin da wata Grace Fedelis ta tambaye shi idan shi ma namijin da ya dace a aura ne, matashin wanda ya kammala jami’ar Joseph Sarwuan Tarka, ya ce shi ma yana son hadaddiyar mace saboda iliminsa da kuma dukiyarsa.
Ya ce saboda yanayin kyawunsa, yanayin kamalarsa, iliminsa, aikinsa, yadda yake samun kudi kamar noma da kasuwanci tare da sauran abubuwa, yana tunanin ya dace ya auri haddiyar mace.
Ya ce duk macen da ke son aurensa to wajibi ne ta kasance daga karamar hukumar Logo ko ukum ko Gboko ko Kwande.