An haife ta da wata cuta mai karanci a duniya inda ake zargin su biyu ne kadai ke fama da wannan cutar. Lalurar tana hana su yin kiba sakamakon rashin samun damar adana abinci a jikinsu, Information.ng ta ruwaito.
Ta kasance bata da kitse ko kadan a jikinta hakan yasa bata da wani nauyi. An nada mata sunan mace mafi muni a duniya a wani bidiyon YouTube inda masu sharhi su ka dinga sukarta.
KU KARANTA: Bella Hadid: Mace mafi kyau a duniya
Akwai wadanda su ka shawarceta da tayi gaggawar halaka kanta ta huta, amma ta ki amsar shawarar su.
Haka ta ba kanta da sauran mutane masu makamanciyar matsalarta kwarin gwiwa akan cewa kada su yarda maganar jama’a tayi tasiri akan su.
Tana daya daga cikin manyan masu ba jama’a kwarin gwiwa a duniya. Ga hotunanta.
Jyoti Amge: Mace mafi ƙanƙanta a duniya, sawu biyu ne tsawonta
Jyoti Amge ita ce ‘yar kasar indiyar da ta shiga cikin littafin tarihi na Guiness a shekarar 2009, inda aka tabbatar da cewa ita ce mace mai rai mafi gajarta a duniya kasancewar tsawonta 61.95cm, wato sawu biyu, guiness world record ta ruwaito.
Bayan shekaru biyu, lokacin ta cika shekaru 17 a duniya, an kara gwada tsayinta inda aka gano ta k su 62.8cm wato sawu biyu da inci 0.72, hakan yasa aka kara tabbatar da cewa ita ce mace mai rai mafi gajarta a duniya.
Yanzu shekarunta 28, inda fiye da shekaru goma da gwada ta tana nan da tsawon da aka san ta da shi.
Yanzu tana shiga shirye-shirmen finafinai inda har ta fito a wani fim din dodannin Amurka mai suna Freak Show wanda aka haska a ranar 8 ga watan Oktoban 2014.