Hukuma masu yaki da ‘yan fasa kwauri na bukatar hadin kan Yan sanda
Bashir Hamisu shugaban hukuma masu yaki da fasa kwauri na Zon B yayi kira ga hukumar Yan sanda dasu hada Kai wajan dakile shige da fice na haramtattun kayayyaki da wasu miyagun ayyuka a garuruwan mu.
Yayi wannan Kira ne lokacin da yakai ziyar ofishin Kamaladeen Okunlola shugaban hukumar Yan sanda na Sokoto.
KARANTA:-Wata kotu dake Legas ta yankewa wani mutum zaman gidan kaso har abada
Ya jinjina wa Yan sanda da sauran hukumomi kan jajircewa wajan yaki da haramtattun abubuwa dake kai kawo cikin kasa.
Yace hadin guiwar ya kara rage yawan miyagun ayyuka da akeyi a kasar kuma ya kara dankon zumunci tsakanin hukumomin.
Kamar yadda yadda ya ayyana yace ya kawo ziyara ne don kara habbaka zaman takewa da kuma kara nuna goyon baya don cigaba da kawar da ta’addanci a kasar.
Yace tabbas irin wannan zai rage barna musamman ta fasa kwauri, kuma irin wannan ba karamin abun cigaba bane ga al’umma.
Shugaban hukumar Yan sanda ta Jahar Sokoto Kamaladeen Okunlola yace sauyi yakan zo akai akai a wannan lokaci ba kamar da ba da zakaga wata kiyayya tsakanin Jami’ai.
Akinlola ya shawarci sauran mabiya dasu cigaba da karatu akan aikinsu don samu dabarori da zasuyi anfani da shi wajan ciyar da aikinsu gaba.
Daga karshe dai yayi kira ga kafafen yada labarai dasu cigaba da kawo labarai masu kyau game da hukumomin.