Wasu mazauna garin Ladipo da ke Mushin a jihar Legas sun mutu sakamakon fashewar iskar gas, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a lamarin, Lamarin wanda aka ce ya faru da misalin karfe tara na safiyar ranar Talata.
Ibrahim Farinloye, Ko’odinetan Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa a jihar ta Legas (NEMA), ya ce fashewar ta faru ne a wata cibiyar sayar da kayayyaki ta LPG da ke kan titin Ojekunke, a kasuwar Ladipo Spare.
Ya ce “ zuwa yanzu, mutum hudu lamarin ya shafa uku maza da mace daya (mama Funmi) sun mutu yayin da jariri daya tilo da aka ceto ya rasu kafin a karasa asibiti.
“An riga an kashe gobara amma ana cigaba da fito da gawarwakin mutane.
Hukumar kashe gobara ta jihar, sashin kula da bala’o’i na ‘yan sanda, NEMA da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) sune suke aikin ceto,” in ji shi
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hukumar kashe gobara ta jihar Legas ita ma ta sanar da cewa tana duba lamarin.