Daga Mu’azzam Yakubu Sanka
Hukumar gudanar da aikin hajji ta Nijeriya wato (NAHCON) a takaice, ta baiwa hukumar lura da jin dadin Alhazai ta jihar Kano kyautar yabo wajen zamowa ta biyu a jerin masu kwazo a aikin hajjin da ya Gabata na Shekara ta 2018.
Shugaban hukumar na Kasa, Barista Abdullahi, ne ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki da kuma bukin bada kyaututtuka ga wasu hukumomin kula da jin dadin Alhazai wadan da suka taka rawar gani a aikin hajjin bara wanda ya gudana a birnin Abuja.
Da yake mika kyautar a hannun sakataren hukumar jin dadin Alhazan jihar Kano, Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, wanda Sanata Sahabi Musa ya wakilta, ya taya gwamnatin jihar Kano, da Hukumar Mahajjatan jihar da kuma daukacin ma’aikatan hukumar murna kan wannan kyautar.
Da yake jawabi kan yadda aka tantance wanda ya dace da kyautar, shugaban hukumar, Barista Abdullahi Mukhtar, yace anyi la’akari ne da irin jajircewa da hukumar tayi wajen aiki mai kyau a lokacin ayyukan hajjin bara.
Shugaban ya kara da cewa an zabi hukumar jin dadin Alhazan Kanon ne duba da irin kokarin ta wajen wayar da kan maniyyata da kuma ilmantar dasu kan yadda ya dace ayi aikin hajji, gami da samar da kyakkyawan yanayin zirga-zirga, tsaftar abinci, da’a, tsaro da dai sauransu.
Shima a nasa jawabin martanin, sakataren hukumar lura da jin dadin Alhazan jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, ya nuna jin dadin sa kan lamarin sa’annan ya bada tabbacin kara kaimi wajen yin mai kyau domin samun daman zamowa na daya a akin hajji mai zuwa, in Allah ya Kai mu.