Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya amince da nadin Alhaji Abdulsalam Abdulkadir a matsayin sabon babban sakatare na hukumar jin dadin alhazai ta jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakatariyar yada labaran hukumar Misis Jumoke Alasela ta fitar a Ilorin.
KU KARANTA KUMA Gwamna AbdulRazaq Ya Musanta Korar Ma’aikatan Gwamnati
Ya bayyana cewa nadin ya fara aiki nan take.
Har zuwa nadin nasa, Abdulkadir ya kasance ma’aikacin Chartered Accountant da ke Legas, inji sanarwar.
An haifi sabon shugaban ne a ranar 1 ga watanYuli, 1964, a Unguwar Pakata a karamar hukumar llorin ta Yamma.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa Abdulkadir ya gaji Alhaji AbdulGaniyu Ahmed, wanda AbdulRazaq ya nada a watan Fabrairun 2021. (NAN)/Solacebace.
A Wani Labarin Kuma Muna Da Mata Miliyan 44m, Maza 49m Wadanda Suka Yi Rajistar Zabe – INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa masu kada kuri’a a zaben 2023 wadanda ka yiwa rajistar zabe akwai mata guda miliyan 44,414,846, yayin da maza kuma suka kasance guda miliyan 49,054,162 ne.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Laraba.