Jiya Asabar Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Kaduna ta sanar da kudin aikin hajjinn inda ta ce dukkan maniyyaci zai biya naira 1.549,297,09 kamar yadda Hiukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta aminece. Mai sanya Ido akan ayyukan hukumar Sheikh Hussaini Suleiman Tsoho ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da hukumar ta gudanar, inda yace, maniiyyatan ana jiran su kammala biyan kudaden su kafin ranar 27 ga watan Mayun 2019. A cewarsa, “A ayau muna sanar da kudin aikin hajjin bana a hiukumace kamar yadda hukumaraiki nhajji takasa NAHCON taamincwa maniyyatan jihar Kaduna na naira miliyan 1.549,549,09 da dako wanne maniyyaci zai biya kuma ko wanne maniyyaci zai biya kudin sa kafin ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 2019 kafin mu kuma tuwawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON nan da ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2019. Sheikh Hussaini Suleiman Tsoho ya yi kira ga maniyyatan dasu gaggauta kammala biyan kudin nasu kafin zuwan ranar rufewar. A cewar Sheikh Hussaini Suleiman hukumar aikin hajjin ta kasa NAHCON ya zuwa yanzu ta warewa jihar Kaduna sama da kujeru 6,636 amma maniyyata 3000 tuni suka biya kudadaden su bayan da suka karbi takartun su na biyan kudi. Sheikh Husaaini Sulaiman Tsoho ya kara da cewa, wadnadsuke son su kara komawa aikin ahajjin,na bana, zasu biya karin kudin saudiyya Riyals 2000 daidai da Naira 163,287.09.