Hukumar dake kula da harkokin alhazai ta Najeriya ta ce matakin kasar Saudi Arabia na hana sauran ƙasashen duniya suwa aikin bana wata ƙaddara ce daga Ubangiji.
Cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ua fitar, ya jinjina wa maniyyata aikin hajjin bisa irin hakuri da juriya da suka nuna tun daga shekara ta 2019.
Alhaji Hassan ya ce duk maniyyacin da ba shi da niyyar barin kuɗin shi a hannun hukumar, to ita a shirye take ta mayar masa shi ba tare da wani jinkiri ba.
A ranar Asabar ne dai kasar Saudi Arabia ta sanar da wannan mataki na cewa mazauna kasar ne kawai za su gudanar da aikin hajjin na bana.
Comments 1