Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA ta bayyana cewa ta sake karbar wasu ‘yan Najeriya 175 da suka dawo daga kasar Libya a ranar Alhamis.
An tarbe su ne ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMA) da ke jihar Legas.
Wannan rukunin ya kai jimillar ‘yan Najeriya 333 da aka dawo da su gida Najeriya ta hanyar shirin tallafa wa ‘yan Najeriyar da suka makale a kokarinsu na neman abun dogaro da kai a kasashen waje.
Wadanda aka dawo da su da radin kansu a cikin wannan rukunin sun kunshi manya maza 92, yara maza shida, da jarirai maza tara. Bugu da kari, akwai manya mata 53, yara mata 12, da jarirai mata uku.
Sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Ikeja a cikin jirgin Al Buraq Airline Boeing 737-400 mai lamba 5A-WAC da misalin karfe 21:48 dare.
An tarbe su ne a filin jirgin NAHCO. Tun da farko an dawo da 158, kafin wannan rukunin.