Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta sauya jadawalin gasar neman cin kofin nahiyar da za’ayi a Cote d’Ivoire.
Maimakon shekarar 2023, yanzu hakan ta dage zuwa karin watanni shiida, wato dai zuwa nan da sabuwar shekarar 2024.
Shugaban hukumar Patrice Motsepe ya sanar da dage gasar daga shekarar 2023 zuwa watan Jarairun 2024.
Tun farko an tsara gudanar da gasar ne tsakanin watan Yuni zuwa Yulin 2023, amma an dage saboda fargabar yanayin, don lokaci ne damuna ne da ake mamakon ruwan sama a yankin.
Da yake jawabi a Rabat na kasar Morocco, Shugaban CAF yace dole ne su dauki matakin saboda gudun kasada.
Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da ake dage gasar ta AFCON, bayan da aka dage gasar ta karshe a Kamaru, wanda inda Senegal ta samu nasarar lashe wa bayan doke Masar a bugun fanariti a wasan karshe.