Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama Malam Tukur Mamu a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar ta Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka kama Mamu a Cario, babban birnin Masar, aka dawo da shi Najeriya.
Tsohon mai sasantawa tsakanin ‘yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da kuma iyalan wadanda abin ya shafa, ya ce ya nufi Saudiyya ne a lokacin da aka kama shi aka tsare shi a Masar na tsawon sa’o’i 24.
Daily Trust ta gano cewa yayin da jirgin Egypt Air da ya kai shi da iyalansa ya isa Kano da misalin karfe 1:55 na rana.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, An jibge jami’an DSS a kofar shiga filin jirgin sama na kasa da kasa mintuna kadan kafin jirgin ya sauka.
Karanta kuma: An Tsare Mai Shiga Tsakanin ‘Yan Bindiga Da Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna
An dai lura da cewa jami’an tsaro dauke da manyan makamai wadanda su ma suke tare da wasu sanye da kayan mufti, suna gadi a kofar shiga bangaren na kasa da kasa yayin da motoci uku dauke da lambobin Kano (Hilux biyu da guda daya) dauke da kaya a kofar shiga.
Ba a jima ba fasinja suka fara fitowa daga sashin isowa, daya daga cikin hilux ya matso gaba yayin da jakunkuna suke tahowa, sai Mamu da ‘yan uwansa aka loda su a daya daga cikin motocin guda biyu.
Daga baya dai an gano cewa motocin biyu sun yi gaba sannan motar bus din ta tafi yankin kwalta kafin daga bisani ta kara hadewa tare da sauran biyun.
An kai Mamu da iyalansa a cikin motar bus din bayan an kama su a kofar shiga filin jirgin.
Wani dan uwa ga masu shiga tsakani ya tabbatar da cewa an kama Mamu da iyalansa kuma an kai su Abuja.
Wata majiya a ofishin DSS a Abuja ta kuma tabbatar da cewa an kama Mamun.
A wani labarin kuma: Wike Bai Halacci Ganawar Da Atiku Ya Yi Da Masu Neman Shugabancin PDP Ba
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas bai halarci wani taro ba a ranar Laraba a lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya gana da masu neman takarar shugabancin jam’iyyar a 2023 a gidansa da ke Asokoro a Abuja.
Baya ga Wike, akwai kuma tsoffin shugabannin majalisar dattawa Bukola Saraki da Pius Anyim da kuma gwamna Emmanuel Udom na jihar Akwa Ibom.