By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati a Legas sun kama wasu mutane 60 da ake zargi da yin damfarar ta yanar gizo a yayin bikin bayar da lambar yabo a otal din taro dake Abeokuta a jihar Ogun.
Hukumar EFCC tace bincike ya nuna cewa taron mai taken ‘Peer Youths Awards,’ an shirya shi ne domin bada kyauta ga manyan masu damfarar ta yanar gizo.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kayayyakin da aka kwato daga wajen wadanda ake zargin sun hada da manyan motoci, na’urorin lantarki, kwamfutoci da wayoyin hannu.
Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, a cikin wata sanarwa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fitar, mai taken, ‘EFCC ta kama mutum 60 a daren baiwa ‘yan Yahoo Boys’ Awards Night, ranar Litinin.