By Abbas Yakubu Yaura
An kama wani dan Najeriya dake cikin jerin sunayen hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka Emmanuel Chidiebere a garin Orlu na jihar Imo.
Rundunar shiyyar Enugu ta hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama shi, a cewar wata sanarwa.
DUBA WANNAN LABARIN: 2023: Tsohuwar Kwamishina Ta Sauya Sheka Daga APC Zuwa Jam’iyyar PDP A Jihar Kwara
A cewar mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, hukumar ta FBI na neman dan Najeriyar da laifin hada baki da zamba da kuma karkatar da kudade.
Sanarwar ta kara da cewa, “EFCC ta kama wanda ake zargi a cikin jerin sunayen FBI da ake nema ruwa a jallo a jihar Enugu
“Hukumar EFCC ta shiyyar Enugu, ta kama Emmanuel Dike Chidiebere, wanda ake zargi da hannu a cikin jerin sa-ido na hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, da laifin hada baki, zamba da kuma karkatar da kudade.
“Da yake tabbatar da bayanan sirri, jami’an hukumar a ranar Laraba, 23 ga watan Maris, 2022, yace sun bi sawun wanda ake zargin zuwa karamar hukumar Orlu ta jihar Imo inda aka kama shi.
“Ana zargin Chidiebere da damfarar wasu da abin ya shafa a kasashen Amurka, Cote D’Ivoire da Poland wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba sannan suka shiga karkashin kasa.
“Uku daga cikin abokan aikinsa har yanzu suna hannunsu.”