By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa dake ofishin shiyyar Ilorin, a ranar Alhamis, ta kama wasu mutane 29 da ake zargi da aikata laifukan damfarar yanar gizo da sauran ayyukan zamba a jihar Kwara.
Wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban yada labarai da hulda da jama’a na EFCC Wilson Uwujaren, ta ce an kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban a garin Offa da ke karamar hukumar Offa ta jihar.
Sanarwar ta ce kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu kan ayyukan wadanda ake zargin.
Wadanda ake zargin a cewar sanarwar sun hada da: Sikiru Mustapha, Abdulmartin Olawale, Gbolahan Abdulamin, Abdulfawaz Olakanmi, Tunde Saheed, David Komolafe, Adebayo Ridwan, Oluwatobi Akinbo, Fatimehin Kayode, Ibrahim Zakariya, Olajide Moshood, Ikudaisi Adesoji, Habeeb Adeyemi da Habeeb Adeyemi da kuma Hassan Akorede.
Sauran sun hada da Ahmed Quadri, Olanipekun Ibrahim, Olabisi Ololade, Ahmed Akorede, Wasiu Adesina, Damilola Samsudeen, Olaloye Damilare, Nathaniel Laoshe, Adeniyi Opeyemi, Adebayo Shahajudeen, Segun Ajila, Kehinde Olaniyi da Ibitowa Toyeeb.
Ya ce abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyin hannu, kwamfutar tafi-da-gidanka da kuma motoci.
Uwujaren ya ce wasu daga cikin wadanda ake zargin sun amince da aikata laifin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken da ake yi.