Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC, ta karkame wani wani Ginin asibiti mallakar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dake kan titin Miller Road a cikin birnin Kano.
Tsohon gwamnan jihar Kanon, Wanda ya wakilci shiyar Kano ta Tsakiya a majalissar Dattijan Kasar nan, a shekarar 2011 zuwa 2015.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda Daily Trust ta bayyana cewa, hukumar ta EFCC ta na zargin Tsohon gwamnan ne, kan zargin madakala da wasu kudaden kanan hukumomin jihar da ya kai naira Billiyan 3.08.
A cikin wata takadda kara da wani Lauya Mai suna Barista Mustapha Danjuma ya rubuta, a madadin Eng Abubakar Mai sha’ani, da kuma Alhaji Najumai Garba Kobo, sun zargin Kwankwaso da amsan naira milliyan 70 na kowace karamar hukuma a jihar, Wanda jimullar kudin ya kai naira billiyan 3.08 na zaben, fidda gwani a shekarar 2015.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba bu siyasa a cikin aikin hukumar tace Fina-finai, cewar Afakallah
Idan za’a iya tunawa dai, Kwankwaso ya naimi tsaya takaran shugaban kasa, a inuwar jam’iyar APC a shekarar 2015. wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya doke shi a zaben fidda gwani.
Sai dai daga bisani Sanata Rabi’u Misa ya sauya sheka zuwa Jam’iyar a dawa ta PDP.
Mai Magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar wa da mane ma labarai cewa, hukumar na bincike kan karar da aka shigar.