Jami’an rundunar hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, sun kama wasu mutane 25 da ake zargi da damfarar yanar gizo (wato Yahoo Boys) a jihar Benue.
An kama wadanda ake zargin ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 13 ga watan Yuni shekarar 2022, a wani samame da aka kai a wurare daban-daban a Otukpo, jihar Benue.
Mutane 25 da ake zargin da aka zakulosu daga maboyarsu biyo bayan samun bayanan sirri da ake zarginsu da aikata na zamba ta yanar gizo sun hada da E. Francis, A. Emmanuel, M. Wakili, C. Francis, I. Emmanuel, J. Williams, P. Idoko, M. Itodo , S. Abah, O. Ameh, O. Samson, O. Amuta , and O. Precious. Sauran su ne: O. Solomon, N. Alex , O. Emmanuel, E. Godwin,O. Ochigbo, E. Chukwu, W. Godwin, Y. Elijah, V. Godwin, L. Owoicho, A. Augustine da O. Moses.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da nau’ikan wayoyin hannu da kwamfutoci daban-daban.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara da cewa wadanda ake zargin sun yi bayanai masu amfani kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.