Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Legas sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a jihar ta Legas.
An kama wadanda ake zargin ne a wani samame da suka kai a Kay-Farm Estate, Ishaga a jihar Legas, biyo bayan wasu bayanan sirri da aka samu kan ayyukan mambobin wata kungiyar masu aikata laifuka ta Intanet da ke damfarar intanet.
An bayyana sunayen wadanda aka kama kamar haka Ogunnowo Aderosola, Adebesin Adeyinka, Nkeokelonye Stanley Ifeanyi, Afolabi Babatunde Oluwaseun, Onyeka Nwokoro, Micheal Adedayo Owolabi, Musah Esosa Hakeem, Osim Happiness, Sanusi Timilehin Olawale, Sanusi Timilehin Rasak, Emmanuel Obogo Adeja, Ogunshoni Samuel Osa Eni Owola , Alabi Ajekola Peter, Timilehin Damilola Emmanuel, Egbuno Ifeanyi Favor da Jimoh Oluwapelumi Ibrahim.
Sanarwar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fitar a shafinta na Twitter ta ce an gano wasu kayayyaki kamar motoci, na’urorin hannu, da kwamfyutocin tafi da gidanka bayan kama su.
Ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gabab kotu bayan an kammala bincike.
A wani labari kuma na daban.
Da Dumi-Dumi: Gwamnan Adamawa Ya Zabi Mace A Matsayin Mataimakiyarsa
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya zabi mace Farfesa Kaletapwa Farauta a matsayin mataimakiyarsa a zaben 2023.
A halin yanzu Farfesa Farauta ita ce Mataimakiyar Shugaban Jami’ar Jihar Adamawa da ke Mubi.
A wajen bikin kaddamar da ita a Yola ranar Laraba, Fintiri ya ce an zabi Farfesa Farauta ce bisa gaskiya, rikon amana, da kuma kwazon da take nunawa akan aiki
Ya ce ana sa ran za ta sauke nauyin da ke kanta tare da taka tsantsan da tsoron Allah, baya ga aikin da take ta yi na uwa na kula da gida.
“Zabar ta ya samo asali ne sakamakon korafe-korafe da kuma kididdigar dabaru musamman bukatar kara daukar matan ta hanyar kula da kuma yiwa kowani jinsi adalci in ji shi.
Gwamna Fintiri ya bukaci jam’iyyun adawa da su shiga cikin gwamnatinsa domin ci gaban jihar.
A nata jawabin, Misis Farauta, wadda ta bayyana zaben ta a matsayin wani abin da Allah ya yi, ta godewa Mista Fintiri da kuma jam’iyyar PDP da suka same ta a matsayin wanda ta cancanta.
Yayin da take ba da tabbacin yin hidima cikin aminci, jajircewa, sadaukarwa da kuma tsoron Allah, ta kuma ce : “Za mu yi aiki tukuru don tabbatar da nasarar jam’iyyar mu a duk zabukan da za a yi nan gaba”.
Mrs Farauta, an haife ta ne a ranar 28 ga watan Nuwamba, 1965 a karamar hukumar Numan, ƙwararriyar fasaha ce wadda ta zama mataimakiyar shugabar mata ta farko a yankin Arewa maso Gabas a Jami’ar Jihar Adamawa dake garin Mubi.