Hukumar ya ki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC, ta cire makulli garkame kaddarar tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Kawankwaso, kasa da awanni 48 bayan garkame shi.
Kaddarar dake a cikin birnin kano, a na kyautatazaton cewa, daya daga cikin asibitin ne, wanda Kwankwaso ya sadaukar da shi, domin killace masu dauke da cutar Korona a shekarar 2020.
A cewar majiyar jaridar Dimokuradiyya Wanda kuma ma’aikacine a hukumar EFCC shiyar jihar Kano, ya ce, tun da fari hukumar ta garkame kadaran tsohon gwamnan ne, bayan wani bincike da ta fara, kan wata kara da aka shigar gabanta, wanda ke da alaka da kaddarar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Mutum 14, sun Kone wani Ruga a Kaduna.
A ranar Juma’a, 20 ga watan Agusta, 2021, hukumar EFCC ta Garkame gidan tare da yin wani rubutu, yayin da kasa da kwani biyu sai aka ga Babu rubutun.
Comments 1