By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a jihar Legas, sun sake kama wani da ake zargi da damfarar yanar gizo, Ismailia Mustapha, bisa zargin karkatar da kudaden da aka samu ta haramtacciyar hanya da kuma rike wasu kudaden da ake zarginsa da aikatawa.
Wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na hukumar Wilson Uwujaren ya rabawa manema labarai ta nuna cewa an kama Mompha ne a ranar Litinin.
“A halin yanzu wanda ake zargin ya gurfana a gaban kotu tare da kamfanin sa, Ismalob Global Investment Limited, kan wasu tuhume-tuhume ashirin da biyu da suka shafi zamba ta yanar gizo da kuma badakalar kudi har naira biliyab 32.9bn da EFCC ta kawo masa.” Inji sanarwar.
Idan dai ba a manta ba jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a baya dai an kama Mompha ne a ranar 18 ga watan Oktobar shekarar 2019 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe yayin da ma’aikatan hukumar shige da fice ta Najeriya suka kama shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Dubai.
Ana zargin Mompha da yin amfani da kamfanonin da ya yi wa rajista wajen karbar haramtattun kudade a madadin yaran ‘yahoo’ daga sassa daban-daban na duniya a matsayin kwamishina.
An yi zargin cewa an yi amfani da asusun daya daga cikin kamfanoninsa Ismalob Global Investment Limited Bank, wani kamfani ne na canji wajen karkatar da kudaden da aka samu daga haramtattun ayyuka.
Bincike ya nuna cewa an samu damfara na dalar Amurka $92,412,75 a cikin na’urar IPhone 8 da ake zargin.
Kakakin ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.