Hukumar kula da kwallon kafa ta FA ta tuhumi Arsenal da Manchester City kan rashin iya sarrafa ‘yan wasansu a wasan da kungiyoyin biyu suka yi a gasar Premier ranar Laraba.
Man City ta samu maki uku masu mahimmanci a kan Arsenal a Emirates a wasan da suka tashi 3-1. Daily Post ta ruwaito.
KU KARANTA: Gwamna Abiodun ya bukaci yan jihar su ci gaba da amfani da tsohon kudi
Sakamakon ya motsa kungiyar Pep Guardiola zuwa matsayi na daya a kan teburin Premier da bambancin kwallaye a gaban Arsenal mai matsayi na biyu.
Koda yake har yanzu mutanen Mikel Arteta suna da wasa a hannu.
Sai dai a yanzu hukumar ta FA ta tuhumi kungiyoyin biyu kan wasu abubuwa da suka faru a yayin karawar.
An tuhumi Arsenal da Manchester City bayan ‘yan wasansu sun kewaye jami’in wasan a lokuta daban-daban yayin wasan Premier ranar Laraba 15 ga Fabrairu. Kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ana zargin kungiyoyin biyu sun kasa tabbatar da cewa ‘yan wasan nasu sun gudanar da ayyukansu cikin tsari, inda ‘yan wasan Arsenal suka zagaye jami’in wasan a minti na 56 da kuma Manchester City a mintuna na 42 da 64.
“Kungiyoyin biyu suna da har zuwa ranar Talata 21 ga Fabrairu don bayar da bahasi mabanbanta.
A wani labarin kuma: Alkawarin da kuka yi na zaben gaskiya da adalci a Imo – PDP
Jam’iyyar PDP a jihar Imo a ranar Juma’a ta bayyana cewa ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fahimci cewa alkawarin da ya dauka na baiwa ‘yan Najeriya zabe na adalci zaici tura a jihar Imo.
Collins Opurozor, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ne ya bayyana haka a Owerri a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida kan halin da kasa ke ciki, hari na uku da aka kai wa kakakin jam’iyyar CUPP, Ikenga Ugochiyere a gida, da kuma kashe-kashen wadanda ba su ji ba ba su gani ba a gidan sa.