Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN ta dakatar da wasu ma’aikatanta bisa laifin karbar na goro a hannun fasinjoji
FAAN, a cikin wata sanarwa da babbar jami’ar kula da harkokin kamfanonin jiragen sama Misis Henrietta Yakubu ta fitar, ta ce dakatarwar ta biyo bayan kudirin hukumar na kawar da manyan jami’an da ke da alaka da karbar cin hanci a filayen jiragen sama na kasa baki daya .
FAAN ta ce ta kama tare da dakatar da jami’an da aka kama suna karbar wani na goro a hannun wani fasinja a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Sanarwar ta kara da cewa, jami’an ma’aikatan sashen tsaron jiragen sama ne da kuma masu hidima na hukumar FAAN abun ya shafa.
Ta ce nan take aka dakatar da su, yayin da aka kwace katin shaidar su na aiki tare da hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS).
FAAN ta ce an dauki matakin ne domin yazamo izina ga wasu miyagun jami’anta da ke kokarin bata sunan kasar nan.