Hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC ta bayyana cewa, an yi asarar akalla rayuka 3,648 a hadurran hanyoyi daban-daban da suka kai 7,5467 a fadin kasar nan, tsakanin watan Janairu shekararan zuwa watan Yuli.
Jami’in wayar da Kan Jama’a na Hukumar, Mista Bisi Kazeem, ne ya bayyana hakan, lokacin da ya zanta da Kamfanin Dillancin Labarain kasar nan NAN a yau Litinin a Abuja, inda ya ce, mutane 22,187 ne suka samu munanan raunuka a hadarurrikan.
“Tsakanin watan Janairu zuwa Yulin Shekarar 2021, hukumar ta Sami rahoton hadarruka 7,567; daga cikin wannan adadin, mutane 1,864 sun mutu, yayin da mutane 4,774 suka Sami rauni mai tsanani, mutane 929 Kuma sukasmi kananan raunika.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abun da yakamata Yan fim mata su kiyaye, Fati Gwammaja
Kazalika ya Kara da cewa,”A watan Janairu zuwa Yulin Shekarar 2021, mutane 3,648 sun mutu, yayin da mutane 22,187 suka tsira daga hadarin tare da raunika daban -daban,” inji shi.
Kazeem ya ce, hukumar ta kuma Sami rahotan aikata laifuka daban-daban har guda 410,754 a cikin shekarar nan, imd al’uma ya Kara da cewa, an gurfanar da Mutum 369,436 cikin su, yayin da aka yankewa 3,165 hukunci.