Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa FRSC ta sanar da masu ababen hawa da ke tafiya da dawowa daga Kudu maso Yamma ta hanyar Kabba zuwa Omuo na jihar Ekiti, da su Kula matuka sabida lalacewar Babban hanyar Tarayya ta yankin Iyamoye na Jihar Kogi.
Jami’in wayar da kan Jama’a na Hukumar, CPEO Mista Bisi Kazeem, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi a Abuja.
Kazeem ya ce, hakan ya hana zirga -zirgar ababen hawa a yankin kamar yadda ya kamata.
“Dangane da abin da ya gabata, an shawarci masu ababen hawa, matafiya, da sauran jama’a da su yi amfani da wata hanya daga Ekiti wacce ita ce: Ikare/Ayerel/Kabba/Lokoja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Saffarar Miyagun Kwayoyi sunyi Garkuwa da Jami’in Hukumar NDLEA a Benue
“Ko Kuma wata hanya da ta taso daga Lokoja ta nufi Kabba/Aiyere/Ikare/Akoko, Lokoja/Kabba/Egbe/Omuaran/Ogidi/Ikare madadin hanya zuwa ko dawowa daga Kudu maso Yamma.”
Kazalika ya ce, “Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya tuni ta fara aiki da matakan da suka dace, don gyara hanyar.” A cewar shi.