Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) reshen Jihar Sokoto, ta kama babura 35 marasa rajista a jihar.
Da yake jawabi Kwamandan sashin, Kabiru Nadabo, ya ce kamen ya yi daidai da umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na cewa kada a bari baburan da ba su da rajista su rika bin hanya.
Nadabo ya ce za a tsawaita aikin a wuraren da ‘yan bindiga ke kai hare-hare.
Sai dai kwamandan ya bayyana cewa za a saki baburan ga masu su da zarar sun kammala rajistar ababen hawan.
Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Kafa Dokar ta ɓaci a Karu, Jahar Nasarawa
Ya kara da cewa rundunar zatayi aiki da hukumar tattara kudaden shiga na cikin gida don tabbatar da cewa an saukaka hanyoyin yin rajista ga masu ababen hawa dake fadin jihar.
A wani labarin kuma
Zaben 2023: Tinubu ne kadai mafita ga Najeriya – Oluwo
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi, ya bayyana Bola Ahmed Tinubu, na jam’iyyar APC a matsayin mafita ga kalubalen Najeriya.
Ya kuma bayyana Tinubu a matsayin wanda ya hada kai da ayyukansa suka yi tasiri wajen wada Najeriya wuri guda.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alli Ibraheem, babban sakataren yada labaransa, Oba Akanbi ya bayyana cewa a matsayinsa na dan Najeriya, Tinubu ya mayar da jihar Legas ta zama abin koyi ga sauran Jihohin kasar.
A cewarsa, “Tinubu dan Najeriya ne da aka wulakanta shi. Irin nasarorin da ya samu wajen mayar da jihar Legas tamkar wani katafaren ido, abin yabo ne matuka, Amanar Najeriya a hannunsa yakamata ya zauna, Za ku ga abin mamaki idan aka bashi dama”
Yayin da yake rokon wadanda suka yi Allah wadai da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Oluwo ya kara da cewa mulki ba shi da alaka da shekaru.
“Yawancin wadanda ke kalubalantar Tinubu na da al’amuran kashin kansu. Mutane da yawa suna cewa yana da girman kai domin yana faɗin gaskiya.
“Mutane suna iya tunanin shi mai girman kai ne domin yana faɗin gaskiya. Duk wanda ya fadi gaskiya an shar’anta shi da girman kai. Mutane suna cewa ni ma mai girman kai ne. Domin ina ƙaunar gaskiya kuma ina fadin ta.
“A ba shi Najeriya ya yi mulki ya rike, Zai yi abun al’ajabi kafin ka wani lokaci,” in ji shi