By Abbas Yakubu Yaura
A wani yunkuri na duba hadarurrukan mota a jihar Taraba, kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a jihar Taraba, Selina Williams, a ranar Juma’a, ta ce rundunar ta kammala shirye-shiryen kakkabe motocin da ba su da na’urorin da suka dace na kayyade iyakar gudu da kuma tsofaffin lambobi.
Williams ta bayyana hakan ne a wata zantawa da ta yi da wakilinmu a Jalingo.
Kwamandan sashin ta ce matakin dage irin wadannan motoci ya zama wajibi ne biyo bayan karuwar hadurran da ake samu a hanyoyin saboda wuce gona da iri da kuma wasu laifukan da suka shafi ababen hawa.
Ta ce, “Rundunar ta kammala shirin dakile duk wasu motocin da ba su da na’urorin kayyade iyakar gudu da kuma tsofaffin lambobi domin dakile hadurran kan hanya.
“Za kuma mu kame motocin da ke yin lodi fiye da kima da sauran laifuffukan cunkoson ababen hawa domin rage yawan hadurran tituna,” in ji ta.
Williams ta bukaci masu ababen hawa a jihar da su rika shiga yanar gizo don samun na’urorin da za su iya kayyade saurin gudu don gujewa fushin doka ta kama su.
Kazalika ta shawarci masu siyar da na’urorin kayyade saurin gudu da su kafa sana’o’i a Taraba domin samun saukin masu ababen hawa a jihar.