Sashen hukumar kula da hadurra FRSC reshen garin Daura, ta bayyana cewa za ta fara gudanar da taron wayar da kan direbobi dangane da saba dokokin tuki a jihar na wata guda.
Malam Tijani Iliyasu, Kwamandan FRSC din na yankin, shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a garin Daura a ranar Alhamis.
Ya tabbatar da cewa za su gudanar da kamfen din ganin sun wayar da kan Direbobi da fasinjoji dangane da hatsarin da yake akwai a cikin gudun wuce kima, da tukin ganganci, da dankarawa mota kaya mai yawa, tare da hada fasinjoji da dabbobi duk a mota daya.
Illiyasu ya ce za su gudanar da taron wayar da kan jama’a ne a wuraren da al’umma ke taruwa kamar irin su kasuwanni, wuraren shakatawa, tasoshin mota, masallatai, da kuma makarantu da kan iyakoki.