Hukumar aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta ba kamfanonin jigilar alhazai wa’adin zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba da su mika bukatarsu na neman aikin jigilar alhazai a shekara mai zuwa ta shafin intanet na NAHCON ko kuma su rasa gurbin yin aikin.
Jami’ar watsa labaran hukumar NAHCON, Misis Fatima Usara, ta bayyana haka a sanarwar da ta raba wa manema labarai bayan da suka kammala taro a kan shirye shiryen aikin hajji na shekarar 2020 yau Laraba a Abuja.
Ta kuma kara da cewa, an yi haka ne don a kauce wa matsalolin da alhazai masu bin jirgin yawo suka fuskanta a yayin aikin hajin shekarar 2019.