Hukumar lura da aikin Hajji ta kasa wato NAHCON, a ranar Talata ta koma Hedikwarta na dindindin a hukumance wanda ke Hajj House wanda yake Metro Plaza a da Abuja.
Hukumar NAHCON din ta tabbatar da hakan ne a shafinta na Twitter. Shi dai sabon Hedikwatar hukumar sun same shi a cikin shekarar 2017.
Da take tabbatar da labarin, Shugabar sashen hulda da jama’a na hukumar, Hajiya Fatima Usara, ta ce sabon ofishi yana Zakaria Maimalari Street, dake Central Business District a Abuja.
Usara ta ce samar da wurin ya sanya hukumar ta kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 2.4 wanda ya kwashe kashi 97.6 na kudin, a yayin da gwamnatin tarayya ta ba da naira miliyan 587 wanda ya dauki kashi 2.4.