By Ishaq Dabai
Hukumar hana fasa kwauri ta Jihar Kano daJigawa NCS, a ranar Alhamis tace ta mika katan guda 185 na magungunan da ba a yi musu rajista ba da kudinsu ya kai Naira miliyan 200 ga Hukumar Kula da ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC.
Kwanturolan rundunar, Mista Suleiman Umar, shine wanda ya mika magungunan ga shugaban gudanar wa na hukumar NAFDAC na jihar Kano, Mista Shaba Muhammad.
Ya kara da cewa, rundunar ta kwace magungunan daga hannun masu fasa kwaurin daga watan Yuli zuwa yau.
“Yawancin laifukan da ake aikatawa ana yin su ne a ƙarƙashin rinjayar waɗannan miyagun kwayoyi, za mu ci gaba da dakatar da shi ko ta halin kaka, ”in ji shi.sannan Umar ya ba da tabbacin cewa hukumar fasa kwauri za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na aiwatarwa tare da taka tsantsan, dangane da bayanan sirri na aiki.
Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bada hadin kai wajen yin hidima ta yadda za a toshe tattalin arzikin masu fasa kwauri da kare lafiyar mutane.
A nasa jawabin, mai kula da NAFDAC ya yaba da hadin kan da ke akwai tsakanin kungiyarsa da hukumar hana fasa kwauri wajen magance zirga zirgar miyagun kwayoyi a kasar nan.
Muhammad ya ce, “kun kubutar da mutane da yawa daga hatsarin da wadannan magunguna suke da shi idan har sun yadu,” in ji Muhammad, ya kuma bukaci mutane da su tona asirin masu safarar miyagun kwayoyi a duk sanda sukayi arba dasu.