Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa da ke buga wasan kati mai suna karta a Kano.
An kama matasan ne a garin Warawa suna “bata lokacinsu” suna buga wasan katin maimakon yin amfani da lokacinsu don yin sana’a mai inganci.
Don haka hukumar ta raba musu wasu surori na Alkur’ani tare da umarce su da su karanta.
“Hukumar a garin Warawa, a karkashin babban Kwamandan hukumar ta Hisbah Dr Muhammad Haroon Ibn Sina, sun kama wasu matasa da sukaebata lokacinsu wajen wasan karta wato (Whot).
“Saboda haka ofishin sashen ya raba musu wasu surori na Alkur’ani mai girma don karantawa kuma don su amfani da lokacin,” in ji wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na hukuamr Hisbah.
A cikin watan Agusta ne hukumar Hisbah ta haramta aje butum-butumi a jihar, inda ta ce hakan na inganta bautar gumaka ne.
“Musulunci ya haramta bautar gumaka. Yana da kai shi ma yana da kai, kamar mutum ne,” in ji babban kwamandan, Ibn Sina.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A ‘yan watannin da suka gabata ma hukumar ta Hisbah ta kama wasu samari da suka yi aski mai wani salo na askin marasa kirki a jihar.