By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta bukaci mazauna jihar dasu tabbatar da tsaftar muhalli da kuma kula da makabartu a yankunansu.
Malam Ibrahim Dahiru, Kwamandan Hisbah shine wanda ya bayyana hakan a wata hira daya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Asabar a garin Dutse.
Dahiru yace, ya kamata makabartar ta kasance tsaftataccen muhalli mai tsarki, ba tare da wani datti ba, yana mai jaddada cewa dole ne a kiyaye shi yadda ya kamata, a yi katanga don kiyaye kutsawa cikin ta.
Kwamandan ya koka da yadda wasu makabartu ke tabarbarewa musamman a yankunan karkara saboda rashin tsaftace su.
“Abin damuwa ne cewa bama ba da kulawar da ake bukata ga makabartu ta hanyar tsaftace muhallin wurin na yau da kullun.
“Wasu daga cikin makabartun ciyawa ta mamaye, kuma wannan ya sa da rana kawai mutane suke iya binne gawa saboda tsoron kada dabbobi masu rarrafe su mamaye su.
A cewarsa, ya kamata mutane su yi kokarin kyautata makabartu domin ita ce wurin hutawarsu.sannan ya kamata ace “Akalla mazauna yankuna su tabbatar sun cire ciyawa sau uku a shekara a makabartarsu,” in ji shi.
Kwamandan ya jaddada bukatar al’umma da malaman addini da gwamnati su wayar da kan jama’a kan mahimmancin tsaftar makabartu.
Kazalika Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kwamandan ya bukaci masu hannu da shuni dasu taimaka wajen samar da shingen wajen katange makabartu a yankunansu, sannan Dahiru ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi dasu hada kai da masu aikin sa kai don kare shi daga kutsawa.