.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa maza da mata a wani taron bikin da ke gudana birnin bisa zargin aikata rashin da’a da kuma sanya tufafin da bai dace ba.
An ruwaito cewa an kama kimanin matasa 78, maza da mata a yayin farmakin na hisbah.
Babban daraktan hukumar Hisbah ta Kano, Haruna Ibn Sina ya shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa ba a kama matasan ba, da laifin yin auren jinsi, kamar yadda wasu ke yada wa.
Wadanda ake zargin dai sun kasance ne a wani wurin taron da ake kira ‘White House’ da ke unguwar Nassarawa GRA a Kano.
“Lokacin da muka samu rahoton mun je can kuma ba mu iya tabbatar da cewa suna auren jinsi daya ba ne, amma mun kama su a cikin wani yanayi na rashin da’a wadanda suka hadar da maza da mata,” in ji kwamandan Hisbah.
Ya ce wadanda ake zargin sun kuma musanta cewa sun halarci wani taron auren jinsi, amma sun ce, suna bikin ranar haihuwar takwarorinsu.
Kwamandan Hisbah ya kara da cewa a halin yanzu duk wadanda aka kama suna hannun hukumar a lokacin da ake gabatar da wannan rahoton.