By Ishaq Dabai
Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifukan ta (ICPC) ta gurfanar da tsohon Shugaban Kwamitin Bincike na Musamman na Shugaban Kasa don Maido da Dukiyar Jama’a (SPIP), Mista Okoi Ofem Obono-Obla, bisa zargin samunsa da yin jabun takardu satifiket.
Hukumar, tanayi masa tuhume-tuhume guda biyu da aka shigar a sashin shari’a na Jos na Babbar Kotun Jihar Filato, taci gaba da zargin cewa tsohon shugaban SPIP ya gabatar da sakamakon bogi a Adabin Ingilishi ga Jami’ar Jos, wanda ya sami damar karanta doka.
Laifin da aka shigar gaban Mai Shari’a CL Dabup, ya bayyana cewa yayin da Obono-Obla bai zauna a matakin kammala Babban Takaddar Shaida (GCE) a Adabin Ingilishi a shekarar 1982 ba, ya gabatar da sakamakon GCE iri ɗaya ga Jami’ar Jos, a shekarar 1985 , dauke da maki shida (6 credit) daga Kwalejin Mary Knoll,ta Ogoja.An kuma cigaba da zargin shi da aikata laifin daya saba da hukunci a karkashin sashi na 366 na dokar manyan laifuka na jihar Filato.
Obono-Obla ya shigar da roko bashi da laifi akan kowanne daga cikin tuhume tuhumen biyu da akeyi masa lokacin da aka karanto masa, bayan haka lauyan sa, M.A Agara, ya shigar da kara yana rokon kotu data bayar da belin sa bisa sanin kan sa.
A baya Agara ya shigar da kara yana kalubalantar hurumin kotun a kan lamarin tare da zargin mai gabatar da kara da kawo gurbataccen tuhuma a gaban kotun tare da rokon kotun da kar ta bari a karanta wa wanda ake kara laifin.
Babban Lauyan hukumar ta ICPC, Henry Emore, wanda yaki amincewa da bukatar dake kalubalantar ikon kotun, ya gabatar da cewa an gurfanar da wanda ake kara a gaban kotu saboda laifin yin jabun takardu (satifiket) a Jos inda kotun ke zama.Sai dai bai yi adawa da bukatar belin ba, amma ya bukaci kotun da ta shigar da shi beli kan tsauraran sharudda.
Mai shari’a Dabup, a hukuncin data yanke kan bukatar belin, ta shigar da Obono-Obla beli akan kudi naira miliyan daya tare da mutum daya da zai tsaya mata.) Ta kuma yanke hukuncin cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance yana zaune a cikin hurumin kotun kuma dole ne ya gabatar da takaddun shaida ciki har da takardar shaidar biyan haraji dake nuna shaidar biyan kudin na tsawon shekaru uku. sannan ta dage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba 2021.
Comments 1